Mayakan daular Muslunci ta IS sun kakkabo wani jirgin yakin kasar Syria a ranar Lahdi a gundumar Deir al-Zour dake gabashin kasar. Wannan ne karon farko da kungiyar IS ta samu zarafin kakkabo wani jirgin yaki tun lokacin da ta kwace manyan wurare a wannan yankin mai arzikin man fetur, in ji kungiyar kare hakkin dan adam ta kasar Syria (OSDH).
An gano jirgin yakin a lokacin da yake tarwatsewa kan wani tsaunin dake birnin Deir al-Zour, bayan da kungiyar IS ta harbo shi, in ji OSDH, tare da kara da cewa, sojojin saman kasar Syria sun kai hare-hare ta sama fiye da ashirin a tsakiyar dare kan mayakan IS a Hwaijat al-Saqer, dake kewayen Deir al-Zour. Hare-haren kuma sun kashe a kalla mayakan IS goma sha shida, aka kuma jikkata wasu da dama, a cewar wasu majiyoyi masu tushe. (Maman Ada)