in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan IS sun lalata wurin tarihi a garin Palmyra
2015-08-24 10:32:31 cri

Rahotanni daga kasar Syria na cewa, mayakan IS sun tarwatsa wurin Ibada na Baal Shamin mai dogon tarihi da ke birnin Palmyra na kasar Syria.

Kungiyar kula da hakkin bil-adam ta kasar Syria ta bayyana cewa, mayakan sun daddasa nakiyoyi ne a wurin Ibadar kafin daga bisani su cinna masa wuta.

Bayanai na nuna cewa, tun lokacin da suka kwace garin, mayakan suka rika kashe sojojin gwamnati da kuma mutanen da ake zargin suna yiwa gwamnatin aiki a bainar jama'a. Sun kuma lalata gidan yarin sojin nan da ya yi kaurin suna da kuma kaburbura da dama da ke garin.

Tun a ranar 20 ga watan Mayun wannan shekarar ce, mayakan na IS suka kwace garin na Palymra ko kuma Tadmur, inda a baya-bayan suka halaka Khaled Asaad, wani fitaccen mai nazarin kayayyakin tarihi 'dan kasar Syria wanda ya shafe kusan tsawon rayuwarsa a garin Palmyra yana nazarin wuraren tarihi da ke garin.

Kafin wannan rikici na kasar Syria dai, masana daga sassan daban-daban na duniya a fanni bincike da nazarin kayayyaki da wuraren tarihi ne ke yin turuwa zuwa kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China