in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi shawarwari tsakanin Sin da Amurka kan tsaro da sa ido kan neman damarar makamai
2015-02-03 14:40:58 cri

Kasashen Sin da Amurka sun gudanar a ranar Litinin da zaman shawarwari karo na bakwai kan dabarun tsaro da sanya ido kan neman damarar makamai daga dukkan fannoni, in ji ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin.

Wannan taro ya samu jagoranci cikin hadin gwiwa tsakanin mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Li Baodong da madam Rose Gottemoeller, karamar sakatariyar kasar Amurka dake kula da damarar makamai da harkokin tsaron kasa da kasa.

Bangarorin biyu sun yi musanyar ra'ayoyinsu kan tsaron kasa da kasa, huldar dangantaka ta fuskar tsaro tsakanin kasashe, da batun gina wani sabon shirin dangantaka tsakanin manyan kasashe.

Haka kuma bangarorin biyu sun cimma ra'ayin karfafa yin shawarwari, dangantaka da sahihancin yarda da juna da ke dogaro da girmama juna da kuma dangantaka ta moriyar juna, ta yadda za'a bunkasa ci gaba mai tsabta na huldar dangantaka tsakanin Sin da Amurka da kiyaye zaman lafiya cikin hadin gwiwa da dorewar kwanciyar hankali a shiyya shiyya, da ma duniya baki daya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China