A jiya Alhamis ne mambobin kwamitin sulhun suka bayyana damuwa kan irin kalubalen da aiwatar da yarjejeniyar ranar 31 ga watan Decemban 2016 ke fuskanta, inda suka bayyana cewa, wadanda suka rattaba hannu kan yarjejniyar sun gaza cimma matsaya kan wasu daga cikin tsare-tsaren da wasu daga cikinsu suka rattabawa hannu a ranar 27 ga watan Afrilu.
Sun kuma jaddada kira da a gaggawar aiwatar da yarjejeniya da kyakkyawar niyyar, domin shirya aiwatar da sahihin zabe cikin kwanciya hankali da lumana daga nan zuwa Decemban wannan shekarar, wanda zai kai ga mika mulki kamar yadda kundin tsari da kuma kudurin kwamitin na 2348 ya tanada. (Fa'iza Mustapha)