Lu ya bayyana haka ne biyo bayanan kalaman da Boris Johnson, sakataren harkokin wajen kasar Burtaniya ya yi cewa, wai ko yankin Hong Kong zai samu nasara ko a'a a nan gaba wannan na dogaro da iko da 'yanci da hadaddiyar sanarwa ta Sin da Burtaniya ta baiwa yankin. Baya ga haka kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka shi ma ya bayyana cewa, kasar sa ta damu da yadda ake keta yancin bil-Adama da na watsa labaru a Hong Kong.
Lu ya kara da cewa, kalaman da wasu ke yi, ko yankin Hong Kong ya samu nasara ko a'a a cikin shekaru 20 da dawowarsa bangaren kasar Sin, wannan ba batu ne da ya shafi wasu kasashe ba. (Bilkisu)