in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika na fatan samun ci gaba cikin sauri kamar gabashin Asiya
2017-06-30 09:36:38 cri

Shehun malami a jami'ar Peking ta kasar Sin Justin Lin, ya ce Afrika na fatan samun ci gaba cikin sauri kamar yadda yankin gabashin Asiya ya samu bayan yakin duniya na biyu.

Justin Lin wanda shi ne daraktan cibiyar sabbin tsare-tsaren tattalin arziki na jami'ar Peking, ya bayyana haka ne jiya, lokacin da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Kigali, babban birnin Rwanda.

Ya ce, idan kasashen Afrika za su samu taimako daga Sin karkashin hadin gwiwar dake tsakaninsu da kuma shawarar "ziri daya da hanya daya", sannan su samu kamfanonin masu bukatar ma'aikata sosai daga kasar Sin, to akwai fatan kasashen Afrika za su samu ci gaba kamar gabashin Asiya.

Yayin tattaunawar da aka yi a wani bangare na shirye-shiryen taron bankin Afrexim, shehun malamin ya ce, abubuwan da ya zayyana ka iya canza makomar nahiyar Afrika.

Yayin zaman taron a ranar Laraba, Lin ya yi kira ga kasashen Afrika su yi amfani da damar da ke akwai na sarrafa kayayyaki daga sabbin tsare-tsaren masana'antu masu samar da abubuwan da jama'a ke bukata。(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China