in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu ruwa da tsaki na Afrika na tattauna hanyoyin samun ci gaba mai dorewa
2017-05-19 10:58:39 cri

An kaddamar da taron tattauna hanyoyin samar da ci gaba mai dorewa a Afrika a birnin Fez na Morocco.

Karkashin taken taron "musayar bayanan nasarorin don samar da ci gaba mai dorewa a Afrika", mahalarta za su yi musayar bayanai kan matakan da kasashensu suka dauka kan yadda za a cimman manufofin samun dawwamammiyar ci gaban al'umma, inda za a maida hankali kan kasashen Afrika da suka cimma nasarori.

Taron zai kuma bayyana nasarorin da shirin raya al'umma na Morocco ya samu, wanda aka kaddamar shekaru 12 da suka gabata.

Sama da wakilai 500, ciki har da jami'an gwamnatocin kasashen Afrika da kwararru ne za su halarci taron na yini biyu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China