in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta yi kira ga mahukuntan Afirka da su kara mai da hankali ga kiwon lafiyar matasa
2017-06-28 09:51:23 cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta yi kira ga mahukuntan Afirka da su kara mai da hankali, ga tsara manufofin da za su habaka kiwon lafiyar matasa a nahiyar.

Da yake tsokaci yayin taron masu ruwa da tsaki game da kiwon lafiya da aka bude a birnin Kigalin kasar Rwanda, daraktan shiyya na nahiyar Afirka a hukumar ta WHO Matshidiso Moeti, ya ce nahiyar na da bukatar tsare tsare da za su dace da kiwon lafiyar dinbin matasan nahiyar, tare da karfafa masu gwiwar gudanar da tsarin rayuwa, wanda zai dace da kiwon lafiyar su.

Mr. Moeti ya ce, lokaci na kara tsawaita, kuma ana samun sabuwar zuriyar bil'adama, don haka ya zama wajibi a yi kokarin cin gajiya daga albarkatun al'umma, ta hanyar samar da tsarin kiwon lafiya mai nagarta, wanda kuma zai dace da bukatar kowa da kowa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China