in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Botswana na shirin karbar bakuncin wasan kwallon kwando na Netball
2017-06-28 16:12:56 cri

Kasar Botswana na shirin karbar bakuncin wasan kwallon kwando ta Netball ajin matasa mata ta kasa da kasa ta bana. Yanzu haka dai hankula sun karkata ga wannan gasa, yayin da masoya wasan suka shiga dokin zuwan gasar a birnin Gaborone, inda gasar za ta wakana.

Botswana za ta karbi kungiyoyin kasashe da yankuna 19 wadanda za su kara a gasar ta 'yan matasa 'yan kasa da shekaru 21, za kuma a fafata ne tsakanin ranekun 8 zuwa 16 na watan Yulin dake tafe.

Da take karin haske game da hakan, babbar manajar shirye shiryen gasar ta wasan Netball dake tafe, uwar gida Tebogo Kesupile, ta ce kasar ta ta shirya tsaf domin gudanar gasar cikin nasara. Kesupile ta ce kwamitin shirye shirye na iyakacin kokari cikin shekaru 2 da suka gabata, domin ganin an cimma nasarar gudanar gasar.

Yanzu haka dai ana shirin kewayawa da kofin gasar, zuwa birane daban daban da kauyukan dake cikin kasar, a wani mataki na yayata zuwan gasar. An kuma fara sayar da tikitin kallon gasar tun kimanin watanni 2 da suka gabata.

Botswana ta samu zarafi na karbar bakuncin gasar ta bana ne tun shekaru 4 da suka gabata daga hukumar INF dake shirya ta, yayin da kuma a hannu guda kungiyar kasar ke ta atisaye, a kokarin su na ganin sun yi rawar gani yayin gasar da za a yi a kasar su. 'Yan wasan sun samu horo a kasar Australia a farkon watan Yunin nan, yanzu kuma suna karkare horo a Afirka ta kudu. A ranar Litinin ne kuma aka bayyana sunayen 'yan wasa mata su 13 na kasar bayan tace 'yan wasan su 23.

Botswana na cikin rukunin C tare da Jamaica, da tsibirin Cook, da Malaysia da kuma kasar Uganda. Rukunin A na da kungiyoyin kasashen New Zealand, da Sri Lanka, da Scotland, da Northern Ireland da Samoa. Yayin da rukunin B ke da kasashen Australia wadda ke rike da kofin gasar, sai kuma Afirka ta kudu, da Barbados da kuma Singapore. Yayin da rukunin D ke da kasar Ingila da Fiji, da Trinidad da Tobago, da Wales da kuma Grenada. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China