in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta bukaci a kara haraji don rage zukar taba sigari a Afrika
2016-08-24 11:09:08 cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bukaci a kara haraji da kuma kuddaden sayar da taba sigari don rage yawan zukar taba sigarin a Afrika. A yayin tattaunawa game da batun harajin na taba sigarin da aka gudanar a Kigali a jiya Talata, jami'in hukumar WHO a Rwanda, mista Olushayo Olu, ya tabbatar da cewar, daukar matakai masu muhimmanci wajen yaki da shan sigari a halin yanzu a Afrika domin kawar da shaye shayen sigari da ya yi muni. Mista Olushayo ya shaida cewa, hayakin sigari yana haddasa rasuwar sama da mutane dubu 6 a duniya a duk shekara, inda ya kara sanar da cewa, kasashen Afrika suna fama da illolin sigari fiye da yadda kasashe masu tasowa suke fama da matsalar a lokacin baya. A don haka ne ya nanata daukar sahihan matakai.

An nuna cewa, karin kudaden sigari da haraji su ne hanyoyi mafi sauki domin rage shan sigari. Wannan taron na kwanaki biyu da WHO ta gayyato sama da mutane 50 daga kasashen Tanzania, da Cote d'Ivoire, da Habasha, da Gambiya, da Equatorial Guinea, da Kenya, da Liberiya, da Ouganda, da Madagaskar, da kuma Saliyo. (Laouali Souleymane)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China