in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO: Daya cikin yaran Somaliya 7 na rasuwa kafin cika shekaru 5
2017-03-08 10:05:53 cri

Daya cikin duk yara kanana 7 da aka haifa a kasar Somaliya na rasuwa kafin cika shekaru 5 a duniya, sakamakon karancin abinci mai gina jiki, dake baiwa cututtuka irin su kyanda damar kassara lafiyar yaran.

Kakakin MDD Farhan Haq ne ya shaidawa manema labarai hakan a jiya Talata. Mr. Haq ya ce, bisa alkaluman da hukumar lafiyar ta MDD ta fitar, kusan rabin al'ummar Somaliya ne kadai ke da iya samun kulawar lafiya da ta dace, yayin da kusan rabin daukacin adadin mata masu juna biyu a kasar ne kadai ke samun tallafin haihuwa daga jami'an lafiya.

Ya ce, matsalar karancin abinci na kara tsananta sakamakon fari dake addabar kasar, matakin da a shekarar 2011 ya haifar da rasuwar kimanin mutane 260,000 a kasar.

Fari na ci gaba da zama gagarumar matsala a Somaliya, baya ga tashe tashen hankula da kasar ta shafe shekara da shekaru tana fuskanta, lamarin da ya jefa mafi akasarin al'ummar ta cikin yanayi na yunwa, da karancin tsaro, tare da matukar bukatar agajin jin kai.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China