Rahotanni daga birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, na cewa, an kwantar da shugaban kasar Zambia Edgar Lungu a asibitin Milpark dake birnin, domin yi masa tiyasa, biyowa bayan matsalar numfashi da ya fuskanta.
An ce, shugaba Edgar ya yanke jiki ya fadi a ranar Lahadi, yayin da yake jawabin tunawa da ranar mata ta duniya. Bayan an duba lafiyar sa a kasar Zambian ne kuma ya yanke shawarar zuwa Afirka ta Kudu domin samun kulawar kwararru.
Wata sanarwa da ofishinsa ya fitar ta ce, shugaban na fama da matsananciyar gajiya, da kuma alamun zazzabin Maleriya.
Lungu ya lashe zaben shugabancin kasar Zambia a watan Janairun da ya gabata ne bayan rasuwar tsohon shugaban kasar Michael Sata. (Saminu)