Wakilin musamman na MDD a kasar Somaliya, Michael Keating, ya yi kakkausar suka game da mummunan harin da aka kaddamar a otel din SYL a Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya, wanda ya hallaka mutane a kalla 13, sannan ya jikkata mutane 20.
Mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric, ya shedawa 'yan jaridu ajiya Laraba cewa, Keating ya bayyana harin na otel din SYL a matsayin kwakkwarar hujja game da irin barnar da ake yiwa al'ummar Somaliya wadanda suke adawa da hare haren ta'addancin kungiyar al-Shabaab.
Dujarric ya ce, harin shi ne karo na 3 da ake kaddamarwa kan otel din SYL daga farkon shekarar 2015.
Bugu da kari Keating ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.(Ahmad Fagam)