in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Ghana ya bukaci sabuwar babbar jojin kasar ta martaba kimar shari'a
2017-06-20 10:37:53 cri

Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya rantsar da Sophia Abena Boafoa Akuffo, a matsayin sabuwar babbar jojin kasar, inda ya umarce ta da ta kasance mai gaskiya, kuma ta yi amfani da ingantaccen ilmin shari'a da take da shi.

Ya ce, abu ne mai muhimmanci ga kasar Ghanan samun mutane masu kima da kwarewar aiki a fanninn shari'a, wadanda za su iya aiwatar da harkokin shari'a bisa ka'ida.

Shugaba Akufo-Addo ya ce, yana da kwarin gwiwa cewa, sabuwar babbar jojin kasar za ta kasance shugaba mai inganci waje kare kima da martabar fannin shari'a.

Shugaban kasar na Ghana ya ce, babbar jojin Akuffo, za ta dora daga inda wanda ta gada ya tsaya wajen daga martabar fannin shari'a, da tabbatar da yin gaskiya, da yin amfani da ci gaban zamani da aka samu a fanni na shari'a, da kuma kafa karin kotuna na musamman domin inganta ayyukan shari'a a kasar bakin daya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China