in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon zai kira taro kan rikicin 'yan gudun hijira dake kwarara zuwa Turai
2015-09-09 10:33:24 cri

Ganin yanayin da ake ciki na kwararar 'yan gudun hijira zuwa kasashen Turai, magatakardan MDD Ban Ki-moon zai shirya wani taron koli game da matsalar 'yan gudun hijira a ranar 30 ga watan Satumba a birnin New York, in ji kakakin mista Ban a ranar Talata.

Bisa damar da aka samu ta amincewa a wannan wata, da maradun ci gaba mai dorewa, sakatare janar na MDD zai gayyaci shugabanni a wani taron koli kan matsalar 'yan gudun hijira da bakin haure, in ji kakakin sakatare janar MDD, Stephane Dujarric.

Mista Ban zai tattauna tare da shugabannin gwamnatocin kasashen Austria, Czech, Jamus, Girka, Hungary, Poland da kuma Slovak game da kwararrar 'yan gudun hijira da bakin haure a kasashen tarayyar Turai, in ji mista Dujarric. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China