in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD na fatan a dauki matakan kaucewa cin zarrafin matan dake gudun hijira
2014-10-29 14:47:40 cri

Kwamitin tsaro na MDD ya nuna bukatarsa a ranar Talata ga kasashe mambobi da su dauki matakai domin kaucewa mata da 'yan matan dake gudun hijira da wadanda suka kaura fadawa cikin azaba da cin zarafi. A cikin kudurin da aka cimma a yayin wani zaman taro da aka kebe kan kare mata da 'yan matan dake gudun hijira da wadanda suka kaura, mambobin kwamitin sulhu sun bayyana cewa, sun yi imanin wadannan mata suna kara fuskantar bazarana da hadura ta wasu hanyoyin keta hakkin dan adam da tauye masu hakkinsu, musammun ma ta bangaren ayyukan azabartawa da fyade da nuna bambancin jinsi, wadanda za'a iyar aikatawa ta matakai daban daban da yanayin lokacin gudun hijira.

Kwamitin ya sake jaddada cewa, nauyi ne da ya rataya ga kasashe mambobi da suka kasance a sahun gaba domin kare al'ummominsu. A cikin sanarwarsa, kwamitin tsaro ya bukaci kasashe mambobi da su dauki nagartattun matakai domin kare mata da 'yan matan dake gudun hijira da wadanda suka kaura daga cin zarafi da gallazawa. Haka kuma ya bukaci kasashe mambobi cewa, idan mata da 'yan mata na fuskantar tashe-tashen hankali da cin zarafi, to ya kamata su kara samun hanyoyin zuwa kotu, musammun ma zurfafa yin bincike, gurfanar gaban kotu da buga masu hukunci mai tsanani ga wadanda ke aikata munanan ayyukan kan mata da 'yan mata. Haka zalika, kasashe mambobi kwamitin sulhu sun yi kira kuma ga dukkan bangarorin dake yaki da su baiwa dukkan 'yan gudun hijira da wadanda suka kaura damar samun taimako da kariyar jin kai cikin walwala da 'yanci. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China