in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin kawance karkashin jagorancin Amurka sun harbo jirgin yakin Syria a Raqqa
2017-06-19 09:45:43 cri

Rundunar sojojin kasar Syria ta bayyana cerwa, sojojin kawance da Amurka ke jagoranta, sun kakkabo wani jirgin yakin kasar dake shawagi a sararin samaniyar birnin Raqqa dake arewacin kasar a jiya Lahadi.

Da yake karin haske cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, babban kwamandan sojojin kasar ta Syria ya ce, dakarun kawance sun kakkabo jirgin yakin kasar ta Syria ne a sararin samaniyar kudancin Rasafeh dake wajen garin birnin Raqqa, yayin da jirgin yakin ke kai hari kan kungiyar mayakan IS.

Sanarwar ta ce, harin na zuwa ne a dai-dai lokacin da sojojin Syria ke kara samun galaba a kan mayakan na IS. Haka kuma sanarwar ta ce, harin ya bankado irin goyon bayan da Amurkar ke baiwa kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar, da ma irin kawancen dake tsakanin Amurkar da kungiyar 'yan ta'addan Daesh ko IS.

A hannu guda kuma rundunar sojojin Syria ta yi gargadin yiwuwar mummunan sakamako biyo bayan wannan harin. Tana mai jaddada cewa, sojojin na Syria ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da kai hare-hare kan kungiyoyin 'yan ta'adda da kuma kokarin maido da zaman lafiya da tsaro a dukkan sassan kasar ta Syria.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China