in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin harkokin wajen kasashe 7 suna tattaunawa kan batun Syria
2017-04-11 10:18:37 cri

Jiya Litinin aka kaddamar da taron ministocin harkokin wajen rukunin kasashe 7 a garin Luca na kasar Italiya, inda mahalarta taron suke tattaunawa kan yanayin da kasar Syria ke ciki a halin yanzu tun bayan da aka kai hari da makamai masu guba a kasar.

Yayin taron da za a shafe kwanaki biyu ana yinsa, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Rex Tillerson ya bayyana cewa, Amurka tana son sake sauke nauyin dake bisa wuyanta domin dakile daukacin mugun laifuffukan dake kawo illa ga fararen hula.

Sakataren harkokin wajen kasar Birtaniya Boris Johnson shi ma ya bukaci kasar Rasha da ta yi hadin gwiwa da sauran kasashen duniya domin warware rikicin Syria ta hanyar siyasa, tare kuma da hana sake aukuwar hare-haren da za a kai da makamai masu guba.

Ministan harkokin wajen kasar Italiya Angelino Alfano ya fayyace cewa, yawancin kasashen Turai suna goyon bayan matakin sojan da Amurka ta dauka a Syria, kana ya yi kira da a gudanar da taro na musamman domin yin musanyar ra'ayi kan batun Syria, ta yadda za a sake maido da shawarwarin neman sulhu a Syria.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China