in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara sabon zagaye na tattaunawar zaman lafiya game rikicin Syria
2017-05-17 10:25:50 cri

Daraktar sashen yada labarai ta MDD dake Geneva ta sanar cewa, a jiya Talata ne aka bude tattaunawar bangarori masu shiga tsakani da nufin lalibo bakin zaren kawo karshen rikicin siyasar kasar Syria da ya shafe shekaru 6 ana fuskanta.

Alessandra Vellucci, ta fadawa manema labarai cewa, tun da misalin karfe 10 na safiyar wannan rana ne tawagar jami'an dake wakiltar gwamnatin Syria suka isa wajen don tattaunawa da wakilin musamman kan rikicin Syria kamar yadda aka tsara tun da farko.

Ta ce, wakilin na musamman zai gana da wakilan kasashen masu shiga tsakani kan rikicin Syria har na tsawon mako guda.

Wakilin musamman na MDD a Syria Staffan de Mistura, a baya bayan nan ya ba da tabbacin cewa, tattaunawar shiga tsakani ta MDDr da wakilan bangarorin 'yan tawayen za ta fi mayar da hankali ne wajen sha'anin mulki, da sabon kundin tsarin mulki, da batun zabe da kuma yaki da ta'addanci.

Jami'in diplomasiyyar ya kara da cewa, tattaunawar da za'a gudanar gajeriyar ce, kuma za ta sha banban da wacce aka saba gudanarwa da ta wannan zagaye, inda ake sa ran kammala ta a ranar Juma'a ko Asabar.

Tattaunawar ta baya bayan nan za ta kasance tattaunawa karo na uku da ka gudanar tsakanin bangarorin masu adawar tun a farkon wannan shekara.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China