in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Binciken da Sin da Afirka ke yi a bangaren aikin gona zai inganta samar da abinci
2015-10-16 09:48:00 cri

Kwararru sun bayyana cewa, binciken hadin gwiwa da kasashen Sin da Afirka ke yi a bangaren aikin gona zai taimaka wajen samar da abinci a nahiyar Afirka.

Babban jami'i a cibiyar binciken hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da ke birnin Nairobi na kasar Kenya John Bosco Njoroge ya shaida wa manema labarai gabanin bikin ranar abinci ta duniya cewa, batun samar da abinci yana daya daga cikin batutuwan da ke zama babbar barazana ga samun ci gaba mai dorewa a nahiyar Afirka. Ko da yake jami'in ya ce, binciken hadin gwiwar da nahiyar ke yi da kasar Sin ya kawar da wannan matsala.

Shirin abinci da aikin gona na MDD wato FAO a takaice ya nuna cewa, akwai kimanin mutane miliyan 245 da ke fama da yunwa da rashin abinci mai gina jiki a yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara. Duk kuwa da imamin da masana suka yi cewa, nahiyar za ta iya ciyar da kanta, muddin gwamnatoci da sassa masu zaman kansu suka kara yawan jarin da suke zubawa a bangaren bincike da kuma sabbin fasahohin da za su kara samar da abinci.

Ita dai wannan cibiya tana mayar da hankali ne kan musayar dabaru da sabbin fasahohin noma na zamani, da kuma hanyoyin da za a bunkasa samar da abinci a nahiyar Afirka.

Bayanai na nuna cewa, kasashen Afirka da dama sun amfana da fasahohin da kasar Sin ta yi amfani da su a bangaren aikin gona wajen kawar da matsalar yunwa a nasu kasashen.

An dai kaddamar da wannan cibiya da ke birnin Nairobi na kasar Kenya ne a shekarar 2014 da nufin magance matsalolin yunwa da kayayyakin abinci masu gina jika a galibin kasashen Afirka.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China