in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana da Faransa sun gana da nufin karfafa dangantakarsu
2017-04-21 10:02:04 cri

Kasar Ghana ta karbi bakuncin taro karo na hudu, tsakaninta da Faransa a birnin Accra, inda kasashen biyu suka nemi karfafa dangantakar dake tsakaninsu.

Ganawar, wadda aka dora a kan nasarorin da aka samu yayin taron kasashen na uku da ya gudana a birnin Paris a bara, ya mai da hankali ne kan manyan batutuwan da suka shafi yankuna da nahiyar Afrika, musammam ma yanayin da ake ciki a Mali da jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da yankin Sahel.

Mukaddashin babban daraktan ma'aikatar harkokin wajen Ghana Edwin Adjei, ya ce, Faransa ta na sauke nauyin dake wuyanta a matsayinta na muhimmiyar abokiyar Ghana ta fuskar ciyar da tattalin arziki gaba.

Ya ce, gwamnatin kasar za ta ci gaba da daukar matakan bunkasa harkokin tattalin arziki, da aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma, domin samun dorewar yanayin kasuwanci da ake ciki a yanzu, kamar yadda yake cikin muhimman shirye-shirye da manufofin gwamnatin game da raya tattalin arziki.

A nasa bangaren, mataimakin sakatare janar na ma'aikatar harkokin waje da raya kasashe na Faransa Laurent Garnier, ya ce Faransa ta dauki Ghana a matsayin muhimmiyar abokiyar huldarta a yankin yammacin Afrika, la'akari da matsayin tattalin arzikinta da tsarinta na siyasa mai dorewa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China