Wata babbar jami'ar kasar Ghana ta ce, kasar a shirye take ta hada kai da kasashen duniya wajen yakar ayyukan ta'addanci.
Shirley Ayorkor Botchwey, ministar harkokin wajen kasar ta ce, Ghana za ta yi iyakar kokarinta wajen goyon bayan kasa da kasa da shiyya shiyya da nahiyoyi domin dakile yaduwar ayyukan ta'addanci.
Da take bayani yayin taron ganawa da jami'an diplomasiyya na Afrika a birnin Accra, Shirley ta ce, kasar ta Ghana ta tura dakarun wanzar da tsaro su 208, da kuma wasu jami'an a matsayin bangaren shirin ECOWAS na wanzar da zaman lafiya a kasar Gambia domin taimakawa kungiyar ta ECOWAS wajen cimma daidaito don tabbatar da dorewa dimokakaradiyya, da tabbatar da zaman lafiya a lokacin sauyin gwamnati a kasar Gambiya.
An shirya taron ganawar ne, domin yin musayar ra'ayoyi wajen karfafa hadin gwiwa da kuma karfafa dangantaka da kasashen duniya.(Ahmad Fagam)