in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya na shirin mai da tsohon ministanta gida domin gurfanar da shi game da badakalar dala biliyan 1.1
2017-06-14 10:04:53 cri

Gwamnatin Nijeriya na daukar dukkan matakan da suka kamata na ganin ta mai da tsohon ministanta na shari'a Mohammed Adoke zuwa kasar, domin yi masa shari'a kan badakalar wasu kudade.

Johnson Ojogbane, lauyan hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasar tu'annuti, wadda kuma ita ce hukumar da za ta gurfanar da tsohon ministan, shi ne ya bayyana haka jiya a Abuja, fadar mulkin kasar.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Mohammed Adoke tare da wasu manyan kamfanonin mai biyu a gaban kotu bisa zarginsu da badakalar kudi dala biliyan 1.1 da kamfanin mai na Malabu.

A ranar karshe da aka dage shari'ar, Alkalin kotun mai shari'a John Tsoho, ya sanya ranar 13 ga watan Yuni a matsayin ranar da za a saurari karar.

Sai dai, Johnson Ojogbane ya bayyanawa manema labarai cewa, an kasa ci gaba da shari'ar saboda EFCC ta kasa samun Adoke da sauran wadanda ake tuhuma.

A cewarsa, gwamnati za ta dauki matakai da hadin gwiwar 'yan sandan kasashen waje domin nemo wadanda ake tuhuma tare da mai da su Nijeriya.

Lauyan ya ce, kotu ta dage sauraron shari'ar zuwa ranar 26 ga watan Oktoba.

A watan Disamban bara ne hukumar EFCC ta gurfanar da wasu mutane 9, ciki har da Mohammed Adoke da laifin sayen lasisin hakar mai

Ana zargin Adoke da tura sama da dala miliyan 800 ba bisa ka'ida ba, domin sayen lasisin ga Dan Etete da kamfanin mai na Malabu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China