in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta yi amfani da fasahar Sin wajen habaka fannin hakar ma'adinai
2017-06-14 09:56:11 cri

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa, za ta yi aiki da fasahar kasar Sin wajen bunkasa da kuma janyo hankalin masu zuba jari daga kasashen ketare a fannin hakar ma'adinai na kasar.

Da yake jawabi a wajen taron shekara shekara karo na farko game da sha'anin ma'adinai a Abuja, babban birnin kasar, mukaddashin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa, tuni aka rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin kwararru na kasashen biyu.

Ya ce, gwamnatin Najeriya tana da burin baiwa kwararru dama da masana fasaha na kasar Sin domin cimma nasarar bunkasa wannan fanni.

Osinbajo ya ce, akwai bukatar kasar Sin ta taimakawa Najeriya wajen zakulo masu zuba jari a fannin kimiyyar hakar ma'adinai domin habaka ci gaban wannan fanni.

A halin yanzu bangaren ma'adinai yana samar da kashi 3 bisa dari ne na tattalin arzikin GDP na kasar, sai dai a cewarsa gwamnatin kasar tana ci gaba da daukar matakan da suka dace domin tabbatar da bunkasa wannan fannin.

Sama da manyan kamfanonin kera kayayyakin aikin hakar ma'adinai 40 na duniya ne aka yi baje kolinsu a babban birnin kasar yayin taron baje kolin nuna kayayyakin na tsawon kwanaki uku.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China