in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an tsaron farin kaya a Najeriya sun damke madugun masu yin garkuwa da mutane
2017-06-13 09:29:14 cri

Jami'an tsaron farin kaya a Najeriya sun kama wasu mutane uku da take zargin da aikata laifukan yin garkuwa da mutane, sannan har da babban madugun masu garkuwa da mutanen, Terwase Akwasa.

Mai magana da yawun hukumar ta DSS Tony Opuiyo, ya fada cikin wata sanarwa da ta iske kamfanin dillancin labarai na Xinhua a birnin Legas cewa, wadanda ake zargin sun hada da Dondo Orsaa, Terhile Mbaloha da Teryima Ihiambe.

A ranar 20 ga watan Afrilu jami'an 'yan sandan Najeriyar suka ayyana Akwasa a matsayin wanda suke nema ruwa a jallo saboda zarginsa da laifin kashe mutanen da ba su ji ba ba su ganui ba da lalata dukiyoyin al'umma na miliyoyin naira a yankunan da dama a jihar Benue dake tsakiyar arewacin kasar.

Yan sandan sun ce, Akwasa shi ne ke da alhakin kashe Denen Igbana, mai ba shawara ga gwamnan jihar Benue Samuel Ortom.

Dama dai gwamnatin jihar ta yi tayin ba da miliyoyin kudade ga duk mutumin da ya bayar da wasu bayanan da za su taimaka a danke Akwasa.

Mutanen 3 dake da alaka da babban madugun, an kama su ne a ranar 9 ga watan Yuni a yankuna daban daban dake karamar hukumar Katsina-Ala a jihar ta Benue.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China