in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Nijeriya na kokarin tsaftace yadda ake amfani da kafofin sada zumunta na zamani
2017-06-14 08:53:53 cri

Gwamnatin Nijeriya ta yi kira ga masu amfani da kafafen sada zumunta su yi amfani da dandalin ta hanyar da ta dace.

Shugaban hukumar kula da kamfanonin sadarwa ta Nijeriya wato NCC Umar Danbatta ne ya yi kiran jiya a Lagos, cibiyar tattalin arzikin kasar, inda ya ce, ya kamata al'ummar kasar su rika amfani da dandalin wajen musayar bayanai tare da shiga harkokin siyasa da zamantakewa da tattalin arzikin kasar.

Sai dai, Umar Danbatta ya ce, ya kamata shiga harkokin ya zama ta yadda za su inganta zaman lafiya da kara gina kasa domin samun ci gaba.

A cewarsa, dokar amfani da kafofin sadarwa ta 2015, ta fayyace irin laifukan da ke da alaka da kafofin tare da tanadin hukunce-hukunce take dokar, yana mai kira ga dukkan al'umma su kiyaye ka'idojin dokar yayin da suke amfani da kafofin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China