in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsarin mulkin Faransa ya ayyana Macron a matsayin sabon shugaban kasar
2017-05-11 09:42:32 cri

Bayan kammala zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Faransa a Lahadin da ya gabata, kwamitin tsrin mulkin kasar ta ayyana Emmanuel Macron a matsayin sabon shugaban kasar da aka zaba jiya Laraba.

Mista Macron wanda ya samu kuri'u da yawansu ya kai kashi 66.01 bisa 100, inda ya doke abokiyar takararsa Marine Le Pen, wadda ta samu kashi 33.9 bisa 100 na kuri'un, kamar yadda kwamitin tsarin mulkin kasar ta bayyana.

Sakamakon zaben ba ya bukatar yin wasu gyare gyare kamar yadda ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Faransan ta wallafa tun a ranar Litinin, zaben ya baiwa sabon shugaban kasar mai shekaru 39 a duniya kuma tsohon ministan tattalin arziki zama shugaban Faransa na 8, kuma shugaban kasar mafi karancin shekaru da aka taba samu a kasar.

Faransawa kusan miliyan 47 ne suka yi rijista a zaben, kuma kusan kashi 25.44 na mutane ba su halarci zaben kasar a zagaye na biyu ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China