in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ofishin jakadancin Sin ya bukaci Faransa ta kiyaye ikon Sinawa a kasar
2017-03-29 11:19:43 cri

Jiya Talata ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Faransa ya bayyana cewa, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin da ofishin jakadancin kasar Sin dake wakilci a Faransa suna mai da hankali sosai kan lamarin game da 'dan sandan kasar ta Faransa ya harbi Basine dake sauka a kasar har lahira a ranar 26 ga wata, kuma gwamnatin kasar Sin ta gabatar da rokon binciken lamarin nan take, kana ta bukaci gwamnatin Faransa da ta dauki wajababbun matakai domin kiyaye tsaro da hakkin halal na Sinawa dake sauka a kasar ta Faransa.

Wata sanarwa da ofishin jakadancin ya fitar a jiya Talata a shafinsa na yanar gizo ta ce, ofishin ya sake gabatar da roko ga mai ba da shawara kan harkokin waje na ministan harkoki cikin gida na Faransa, domin binciken musababbin aukuwar lamarin tare da daukar matakan kiyaye tsaro da hakkin Sinawa dake sauka a kasar.

Sanarwar ta kara da cewa, gwamnatin Faransa ta ce, lamarin ya dame ta, kuma tana kokarin yin bincike, inda ta yi alkawarin kammalawa da wuri. Sa'annan ta yi kira ga Sinawa dake zaune a Faransa da su kara hakuri.

A Jiyan ne kuma ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta sanar da cewa, gwamnatin kasar ta na mai hankali sosai kan kiyaye tsaron Sinawa dake zaune a kasar, tana mai cewa, yanzu haka tana gudanar da bincike kan lamarin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China