in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan ta Kudu zai ziyarci Khartoum
2017-01-03 09:50:28 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sudan ta kudu Deng Alor ya bayyana cewa, shugaban kasarsa Salva Kiir Mayardit, zai kai ziyarar aiki zuwa kasar Sudan nan da 'yan kwanaki masu zuwa.

Alor, ya sanar a jiya Litinin bayan wata wasika wanda shugaba Kiir ya aikewa takwaransa na Sudan Omar al-Bashir, game da huldar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Batun warware rikicin kan iyakokin Sudan da Sudan ta kudun, na daga cikin muhimman batutuwa da ganawar shugabannin biyu za ta fi mayar da hankali.

A watan Satumban shekarar 2012 ne, kasashen biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, wanda ya samu halartar kungiyar tarayyar Afrika, yarjejeniyar da aka kulla ta kunshi hadin gwiwa wajen tabbatar da tsaro, matsayin 'yan kasashen biyu, da kan iyakoki, da tattalin arziki, da kuma sauran baututuwa da suka hada da batun albarkatun mai da kasuwanci. To sai dai kuma, yarjejeniyar ba ta kai ga warware takaddama kan yankin nan na Abyei, da kuma batun shata kan iyakokin kasashen biyu ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China