in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da tarurukan dandalin tattaunawa tsakanin masu masana'antu na kasar Sin da na Afirka a Kenya
2015-07-21 16:15:06 cri

A ranar Litinin ne aka gudanar da dandalin tattaunawa tsakanin masu masana'antu na kasar Sin da na Afirka, taron da bankin ICBC na kasar Sin, da Standard Bank, da dandalin tattaunawa na masu masana'antun kasar Sin suka dauki nauyin shiryawa a birnin Nairobi, fadar mulkin kasar Kenya.

Shugabanni sama da 100 daga bangaren 'yan kasuwa wadanda suka fito daga kasashen Sin da na Afirka ne suka samu halartar taron, inda aka tattauna game da makomar hadin gwiwa tsakanin masu masana'antu na kasar Sin da na Afirka.

Wakiliyarmu Lubabatu na dauke da karin bayani.

An gudanar da jerin tarurukan dandalin ne a kasashen Afirka ta kudu da kuma Kenya, kuma wannan karo a kasar Kenya, an fi maida hankali ne kan bayyanawa masu masana'antu na kasar Sin damar zuba jari da Kenyan ke da su, tare kuma da bayyana wa hukumomin Kenyan, da masana'antun kasar kwarewar masana'antun kasar Sin, da kuma bukatunsu a fannin zuba jari, a wani kokari na karfafa fahimtar juna tsakanin masana'antun kasashen biyu, don share wa masana'antun kasar Sin fagen zuba jari a Kenya.

Ministan harkokin kudi na kasar Kenya Henry K. Rotich, ya ce gwamnatin kasar Kenya za ta sa kaimi wajen zuba jari a fannonin samar da manyan ababen more rayuwa, da makamashi, da zirga-zirga da kuma yawon shakatawa. Kana kasar na maraba da kamfanonin hada-hadar kudi na kasar Sin, da ma sauran masana'antun kasar wajen kokarin zuba jari a kasar, don cimma moriyar juna.

A nasa bangare jakadan kasar Sin a Kenya, Mr. Liu Xianfa, ya bayyana muhimmnacin da taron dandalin ke da shi tsakanin masu masana'antu na sassan biyu, kuma a ganinsa faduwa ta zo daidai da zama, duba da cewa taron ya zo a gabar da kasashen Sin da Kenya ke kokarin hadin gwiwa da juna a fannin makamashi, don haka, ya yi fatan bankin ICBC, zai kasance babban bankin na farko a duniya, wanda zai taka kyakkyawar rawa wajen jagorantar masana'antun kasar Sin a fannin zuba jari a Kenya.

Har wa yau, Mr. Jiang Jianqing, daraktan darektocin bankin ICBC a jawabin da ya gabatar a gun bikin bude taron, ya ce, kasancewarta jagora a kungiyar kasashen gabashin Afirka, Kenya ta kuma zama wata muhimmiyar kasa a Afirka wadda 'ziri daya da hanya daya' da ake kokarin ginawa za su ratsa. Kana taron dandalin na wannan karo zai samar da damar tattaunawa kan wasu muhimman batutuwan da suka hada da hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen biyu, da zuba jari a Afirka, a kokarin ganin a daukaka hadin gwiwar Sin da Kenya.

Shi kuwa a nasa bangaren, babban darektan zartaswa na Standard Bank Ben Kruger, cewa ya yi a matsayinsa na bankin kasuwanci mafi girma a Afirka, kuma abokin hadin gwiwa na bankin ICBC, Standard Bank zai samar wa masana'antun Sin da na Afirka ingantattun hidimoni ta fannin hada-hadar kudi.

A yayin taron, wakilin masu masana'antun na kasar Sin, kana darektan darektocin kamfanin TCL na kasar Sin, Mr. Li Dongsheng, da kuma babban masanin ilmin tattalin arziki a taron dandalin tattaunawar masu masana'antun kasar Sin, Mr. Zhang Weiying, sun tattauna da wakilin CRI, inda Mr. Li Dongsheng ya bayyana cewa dalilin halartar wannan taro shi ne habaka damar kasuwanci ga kamfaninsa a Afirka. Ya ce, kamfaninsa zai kafa masana'anta a yankin da ya dace, don kyautata kwarewar sa a takara tare da sauran takwarorinsa, da kuma kara kason kayayyakin sa a kasuwannin Afirka.

Shi kuwa Mr. Zhang Weiying cewa ya yi kasar Sin da kasashen Afirka na kara hadin gwiwa da juna a fannin hada-hadar kudi, a sanadin hadin gwiwar su an kara karfafa alaka tsakanin sassan biyu a fannonin tattalin arziki da ciniki. A yayin da kamfanonin kasar Sin ke kara zuba jari da gudanar da kasuwanci a Afirka, harkokin hada-hadar kudi ma bai kamata a bar su a baya ba, don haka ya ce hadin gwiwar bangarorin biyu a fannin hada-hadar kudi na da makoma mai kyau.

A gun taron dandalin, ban da bunkasa huldar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen gabashin Afirka, masu masana'antu na kasashen biyu, da kuma masu aikin hada-hadar kudi za su kuma tattauna kan batutuwan da suka shafi samar da wutar lantarki, da manufofi, da dokoki, da kuma hanyoyin hadin gwiwa, wadanda ke daukar hankalin masana'antun kasar Sin da ke da niyyar zuba jari a Kenya. Ban da haka, a yayin taron, bankin ICBC ya kuma cimma yarjejeniya da ma'aikatar kudi ta Kenya, kan raya manyan ababen more rayuwa a kasar. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China