in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tsinci gawar jami'in MDD a Afrika ta kudu
2017-06-06 11:08:37 cri

Ofishin MDD a Afrika ta kudu ya tabbatar a ranar Litinin cewa, an tsinci gawar wani jami'in MDD a wani tsauni na Table Mountain dake birnin Cape Town, jami'in ya bace ne tun a watan Maris.

Charlotte Nikoi, daraktan kula da ma'aikata na hedkwatar ofishin tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF) a birnin New York, ya bace ne a watan Maris a lokacin da yake hutu tare da iyalansa a Cape Town.

Dama dai 'yan sanda sun kaddamar da binciken neman Nikoi, amma ba su same shi ba. A makon jiya, 'yan sanda suka tsinci gawarsa a tsaunin Table Mountain. Bayan wasu gwaje gwaje da aka yi kan gawar, an gano cewar Nikoi ne, dan shekaru 50 da haihuwa dan asalin kasar Ghana.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China