Mai magana da yawun babban sakataren MDD Farhan Haq ya shaidawa taron manema labarai a jiya Jumma'a cewa, wadanda suka tsira sun ba da labarin cewa, motar da mutane 50 din dake ciki a kan hanyarsu ta zuwa Libya ne ta lalace tsakanin biranen Agadez da Dirkou dake hamadar Saharar a yankin arewacin Jamhuriyar Nijar, lamarin da ya cusa su cikin tsananin zafi da karancin ruwan sha, kuma mutane shida ne kadai suka tsira.
Hukumar ta UNHCR ta sake yin kira ga kasashen duniya da su dauki matakan da suka dace don magance yadda jama'a ke kokarin kaura zuwa kasashen waje. Yanzu haka hukumar tana neman taimakon dala miliyan 75.5 don kara agazawa harkokin jin kai da biyan bukatun jama'a a kasar Libya, ciki har da wadanda suka bar muhallansu da masu karbar bakuncinsu gami da 'yan gudun hijira da masu neman mafaka. (Ibrahim)