Bangaren 'yan sadan kasar Burtaniya a jiya Asabar ya ce, a daren ranar an samu abkuwar lamuran tsaro guda uku a birnin London, ciki har da wata babbar mota mai daukar kaya ta ci karo da mutanen dake tafiya a gadar Landan, wanda ya haddasa rasuwar mutane 6.
Bangaren 'yan sandan London ya bayar da sanarwa cewa, yanzu 'yan sandan suna bincike kan lamarun uku da suka faru a gadar Landan, da kasuwar dake dab da gadar, da kuma Vauxhall dake kudu maso yammacin birnin. A cewar bangaren 'yan sandan, an riga an tabbatar da cewa, lamuran biyu hari ne na ta'addanci, a yanzu haka 'yan sanda sun harbe mutanen uku da ake tuhumarsu da hannu a cikin lamuran har hahira.
Kafofin watsa labarun kasar Burtaniya sun ruwaito cewa wadanda suka ganewa idonsu faruwar lamarin sun ce, wata motar daukar kaya ta yi buge masu tafiya a gadar Landan, har ma an kai farmaki kan mutane da wuka, hakan ya rautata mutane da dama.
Bangaren 'yan sandan bai fayyace yadda aka kai farmaki a kasuwar dake dab da gadar London din ba. Amma, a cewarsu, lamarin kai farmaki da wuka da ya faru a Vauxhall ba shi da nasaba da sauran lamura biyu.
Za a shirya zabe a kasar Burtaniya a watan Agusta. Firaministar kasar Theresa May dake yakin neman zabe a sauran wurare ta riga ta komo fadarta cikin gaggawa a daren ranar Asabar din. (Bilkisu)