in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
SADC ta kammala tsarin hanyoyin da za'a bi kan masana'antu
2015-04-28 10:52:38 cri

Ministocin kasashen kungiyar raya kasashen kudancin Afrika SADC sun fara wani taro a Harare a ranar Litinin din nan domin nazarin takardar tsarin dabaru da hanyoyin da za'a bi wajen mai da hankali a kan masana'antu domin azalzala masana'antu a kasashen mambobin kungiyar 15.

Shugaban tawagar ministocin kungiyar kuma ministan harkokin kasashen waje na kasar Zimbabwe Simbarashe Mumbengegwi ya shaida wa mahalarta taron cewa, wannan hanya da za'a tsara za ta fara ne daga wannan shekarar ta 2015 zuwa 2063 a lokacin da yankin zai bukaci mai da masana'antu cikin matakai uku.

Ya ce, wannan tsari ya tabbatar da cewa, tsarin kafa masana'antu da aiwatar da hakan, za'a yi shi ne a matakin kasa baki daya kuma kadan ne za su dogara a kan hadin gwiwwa tsakanin gwamnati da hukumomi masu zaman kansu.

Wannan tsarin ya bayyana manufofi, kalubaloli, ayyukan shiga tsakani, da kuma sakamakon da wadanda za'a fi mai da hankali a kai karkashin manyan shirye-shirye guda uku wato masana'antu, takara da kuma shigar da yankuna a ciki, in ji minista Mumbengegwi. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China