Wannan shi ne karo na 2 da Japan ta sake karbar bakuncin taron kolin G7 bayan shekaru 8. Kasashe da dama za su tattauna batutuwan ciniki, da tattalin arziki na duniya, da batun 'yan gudun hijira da yaki da ta'addanci. Sauran batutuwan sun hada da na sauyin yanayi, da albarkatun ma'adinai, da zaman lafiya da karko a Asiya. Kaza lika bisa wasu manufofi da Japan ke nacewa, an yi hasashen cewa, za a tattauna batun kudancin tekun kasar Sin a yayin taron.
A gobe Juma'a za a gudanar da taron gaman gari na kungiyar ta G7, inda ake sa ran tattauna batun saka jari a fannin ababen more rayuwa. Taron da aka gayyaci shugabannin kasashen Chadi, da Indonesiya, da Sri Lanka don su halarta. Har wa yau babban magatakardar M.D.D. Ban Ki-Moon, da asusun ba da lamuni na duniya, da bankin duniya da sauran kungiyoyin duniya za su tura wakilai don halartar sa.(Bako)