in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron koli na G7 a gabar da masu adawa ke gudanar da zanga-zanga
2015-06-08 11:26:41 cri

An bude taron koli na kungiyar kasashe masu samun saurin bunkasuwa ko G7 a takaice, a fadar Schloss Elmau, dake garin Garmisch-Partenkirchen a kudancin kasar Jamus.

Yayin taron na yini biyu an tattauna batutuwan da suka shafi dangantakar kawancen cinikayya a ketaren tekun Atlantika, da dangantakar Rasha da kasashen yammacin duniya, da batun sauyin yanayi da dai sauransu, a gabar da wasu masu zanga-zanga kimanin su dubu ke jerin gwano nuna adawa da taron.

Kafin bude taron, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, da shugaba Barack Obama na Amurka sun gudanar da wani taron tattaunawa, inda suka bayyana cewa kafin a kai ga aiwatar da yarjejeniyar Minsk ta warware rikicin Ukraine, kamata ya yi kasashen yammacin duniya su ci gaba da aiwatar da takunkumin da suka kakabawa kasar Rasha. Shugaba Obama ya ce kamata ya yi a mai da yaki da kalubalantar Rasha tamkar babban taken taron ne na wannan lokaci.

Sai dai a gabar da taron ke gudana, wasu kungiyoyin dake kasar ta Jamus wadanda ba na gwamnati ba, da wasu jam'iyyun gama kai, da kungiyoyin jama'a sun gudanar da zanga-zanga. Inda suka bayyana rashin gamsuwa da cika alkawuran da taron na G7 ya dauka, game da warware matsalar sauyin yanayi, da rage talauci, suna musu bukatar da a dauki karin matakan kiyaye muhalli, da yaki da talauci a duniya.

'Yan sanda sun yi taho-mu-gama da masu jerin gwanon, inda kuma suka cafke wasu daga cikin su. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China