in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cote d'ivoire: MDD ta nuna gamsuwa game da kawo karshen tarzoma
2017-05-18 10:25:22 cri
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya bayyana gamsuwa game da kawo karshen bore sojojin a kasar Cote d'ivoire, yana mai nuna rashin dacewar tarzomar da sojojin kasar suka yi a 'yan kwanakin da suka gabata.

Cikin wani rahoto da aka gabatar ga manema labarai a jiya Laraba, ofishin MDDr ya bayyana cewa, tarzomar sojoji a Cote d'ivoire ta sabbaba kisan mutane uku, kafin sojojin su amince da dakatar da bore da suka gudanar bisa rashin gamsuwa da yanayin albashin da gwamnatin kasar ke biyan su.

Mr. Guterres, ta bakin kakakin MDDr stephen dujarric, ya jinjinawa gwamnatin kasar ta Cote d'ivoire, bisa kokarin ta na warware takaddamar da ta kunno kai, tare da daukar matakai na wanzar da zaman lafiya a kasar.

Har wa yau ya bayyana cewa, MDD za ta ci gaba da baiwa kasar Cote d'Ivoire goyon baya, domin dorewar zaman lafiya da lumana, wanda yanzu haka ke samun bukasuwa, ciki hadda matakin da MDDr ta dauka, na tura tawagar wanzar da zaman lafiya na ONUCI zuwa kasar, da ma hadin gwiwar da take yi da sauran sassa na abokan hulda a kasar.

Shekaru 13 ke nan tawagar ONUCI ke aiki a Cote d'ivoire, ana kuma sa ran za ta karkare ayyukan ta cikin watan Yuni mai zuwa.

Rahotanni dai sun bayyana cewa, sojojin sun amince da dakatar da boren ne a ranar Talata, suka kuma koma barikokin su, yayin da kuma al'amura ke kara daidaita a biranen abidjan, da bouake, birane mafiya girma a kasar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China