An ce, a madadin gwamnatin kasar, ministan tsaron kasar ya halarci shawarwarin, a karshe dai an cimma daidaito tare da sojoji masu yin bore. Kana sojojin da dama sun tabbatar da cewa, bangarorin biyu sun daddale yarjejeniyar zaman lafiya.
Wani masani game da harkokin gwamnatin kasar Cote d'Ivoire ya bayyana cewa, sojoji masu tada rikicin sun amince da komawa sansanoninsu, kana an dakatar da harbar bindiga a birnin Bouake. Ya ce, bisa yarjejeniyar da aka daddale, ko wane sojojin zai samu kudi dala dubu 19 daga gwamnatin kasar. Wani wakilin sojojin dake halartar shawarwarin ya bayyana cewa, za a fara biya kudin tun daga ranar 16 ga wannan wata. (Zainab)