in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Kasuwar sayayya ta yanar gizo ta samu tagomashi a bara
2017-05-18 09:21:49 cri

Kasuwar sayayyar kayayyaki ta yanar gizo ta samu tagomashi mafi girma a shekarar 2016 da ta gabata, inda kudaden da aka kashe a sashen ya karu, zuwa kaso 39.1 bisa dari. Kaza lika yawan kudaden cinikayyar ya kai kudin Sin RMB yuan tiriliyan 5.3, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 770, kamar dai yadda wani rahoto na wata cibiyar binciken harkokin kasuwanci na kasar Sin ya bayyana.

Wannan fanni na cinikayya ta yanar gizo dai na daukar kaso 14.9 bisa dari, na daukacin sayayyar da al'ummar kasar ta Sin suke yi a duk shekara, wanda kuma hakan ke nuna karuwar kaso 2.2 bisa dari a ko wace shekara.

Rahoton ya kara da cewa, yawan mutanen da suka shiga hada hadar cinikayya a wannan fanni a shekarar ta bara, ya kai mutane miliyan 500, wanda hakan ya nuna ci gaban da aka samu a fannin da kaso 8.6 bisa dari, idan an kwatanta da na shekarar da ta gabata.

Wani abun lura ma shi ne yadda wannan hada hada ta samu bunkasa a yankunan karkarar kasar Sin da kaso 36.6 bisa dari, kuma adadin kudaden da aka kashe a yankunan ya kai RMB yuan biliyan 480 a shekarar ta bara, akwai kuma hasashen cewa adadin zai karu zuwa yuan biliyan 600 a bana. A daya bangaren kuma, hada hadar cinikayya tsakanin sassan kasar Sin da kasashen ketare ta yanar gizo ta karu da kaso 33.3 bisa dari, inda yawan kudaden da aka kashe suka kai yuan tiriliyan 1.2.

Har ila yau, yawan kudaden da manyan kamfanonin aikewa da kayayyaki suka samu a bara wajen ba da hidima ya kai yuan biliyan 400, adadin da shi ma ya karu da kaso 44.6 bisa dari.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China