in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya tsawaita wa'adin aikin tawagarsa a Abyei da watanni 6
2017-05-16 10:18:05 cri

A jiya Litinin kwamitin tsaron MDD ya kada kuri'a da ya samu amincewar dukkan mambobinsa domin tsawaita wa'adin aikin jami'an MDDr dake aikin wanzar da zaman lafiya a yankin Abyei (UNISFA) har zuwa ranar 15 ga watan Nuwamban bana.

Kwamitin mai wakilan kasashe 15 ya nanata cewa, zai ci gaba da yin hadin gwiwa tsakaninsa da gwamnatin Sudan da ta Sudan ta kudu domin ci gaba da aikin wanzar da zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali da kuma kokarin kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu a nan gaba.

Kwamitinn na MDD ya kuma jaddada aniyarsa na ganin cewa, kasashen Sudan da Sudan ta kudu sun gaggauta kafa kwamitin gudanar da mulki ta yankin Abyei, ta yadda za'a iya cimma matsaya don warware takaddamar da ake yi kan yankin mai arzikin mai.

Sudan da Sudan ta kudu sun jima suna takun saka game da yankin na Abyei mai arzikin mai, kuma galibin mazauna yankin 'yan kabilar Arab Mesiria na kasar Sudan ne da kuma kabilar Dinka Ngok na Sudan ta kudu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China