in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya tsawaita wa'adin aikin tawagar UNISFA a yankin Abyei
2015-02-27 09:49:24 cri

Kwamitin tsaron MDD ya amince da tsawaita wa'adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta UNISFA a yankin Abyei mai arzikin mai, yankin da kasashen Sudan da Sudan ta Kudu ke takaddama a kan sa.

Wani kuduri da zauren kwamitin ya amince da zartas da shi ne a jiya Alhamis, ya tabbatar da karin wa'adin tawagar ta UNISFA, ya zuwa 15 ga watan Yulin wannan shekarar da muke ciki.

Kwamitin tsaron dai ya bayyana daukar wannan mataki a matsayin wata hanya ta habaka shawarwari tsakanin sassan biyu, tare da kare rayukan fararen hula. Kaza lika ya bukaci dukkanin masu ruwa da tsaki da su yi aiki tare da MDD a kokarin da ake yi na sake komawa teburin shawara.

Tawagar UNISFA ta fara aiki a yankin na Abyei ne tun a shekarar 2011, bayan barkewar tashin hankali, tsakanin dakarun sojin gwamnatin Sudan da na Sudan ta Kudu game da ikon mallakar yankin. An kuma dorawa tawagar alhakin tabbatar da kwance damarar yaki, tare da wanzar da tsaro a yankin. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China