in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kara wa'adin tawagar UNISFA da ke Abyei
2014-10-15 10:39:56 cri

A ranar Talata 14 ga wata ne kwamitin sulhu na MDD ya kara wa'adin tawagar wanzar da zaman lafiya da ke aikin a yankin Abyei da ke kan iyaka tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu.

Kwamitin mai mambobi 15 ya yanke shawarar kara wa'adin tawagar ta UNISFA ne da karin watanni 4 da rabi wato har zuwa ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2015.

Ya kuma yi kira ga kasashen Sudan da Sudan ta Kudu da su yi kokarin hallara kan kwamitin sa-ido kan yankin na Abyie (AJOC) da ke kula da harkokin tafiyar da mulki a yankin da aka daina jin doriyarsa na kusan sama da shekara guda.

Bugu da kari kwamitin ya yaba da yadda 'yan sanda Sudan da sojojin Sudan ta Kudu ke sintiri a yankin na Abyei, sai dai ya nanata cewa, kamata ya yi a kawar da dakaru kwata-kwata gami da 'yan banga a yankin, in ban da dakarun wanzar da zaman lafiya na wucin gadi na MDD da 'yan sandan Abyei.

An yanke shawarar kara wa'adin tawagar da ke Abyei ne sabado zaben kasar da ke tafe, lamarin da ake ganin na iya haifar da babbar barazana ga zaman lafiya a shiyyar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China