in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu ya kara wa'adin UNISFA dake yankin Abyei
2015-07-15 09:41:28 cri

Kwamitin sulhu na MDD ya kara wa'adin tawagar da ke aikin wanzar da zaman lafiya ta MDD a yankin Abyei da ke kan iyakar kasashen Sudan da Sudan ta Kudu.

Manufar kara wannan wa'adi na tsawon watanni biyar, ita ce baiwa tawagar mai dakaru sama da dubu 4 ci gaba da kare rayukan fararen hula da ke yankin na Abyei mai arzikin man fetur.

Sabon kudurin da kwamitin ya yanke na kara wannan wa'adi wanda zai kare ranar 15 ga watan Yulin shekarar 2015, ya biyo bayan kiraye-kirayen da gwamnatocin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu suka yi ne na ganin a hanzarta kafa gwamnati a yankin na Abyei.

Kwamitin mai mambobi 15 ya kuma yi kira ga gwamnatocin kasashen biyu, da su kafa rundunar 'yan sandan yankin Abyei wadda za ta rika kula da harkokin da suka shafi yankin, ciki har da kare na'urorin mai da ke yankin.

A ranar 27 ga watan Yunin shekarar 2011 ne aka kafa tawagar ta UNISFA sakamakon fadan da ya barke, da kuma karuwar tashin hankali da ke tilastawa mutane barin gidajensu makonni kafin samun 'yancin kan kasar Sudan ta Kudu a shekarar 2011.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China