Jakadan Sin a kasar Syria Qi Qianjin, ya ce kasar sa za ta kara yawan tallafin ta ga kasar Syria, a wani bangare na aiwatar da manufofin jin kai dake kunshe cikin shawarar ziri daya hanya daya.
Mr. Qi Qianjin ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, yayin ganawar sa da shugaban sashen tsare tsare da hadin gwiwar kasa da kasa na Syria Imad Sabouni. Jami'an biyu sun kuma rattaba hannu kan takardun yarjejeniyar samar da tallafin abinci, da sauran kayayyakin jin kai don talllafawa al'ummar Syria.
Kaza lika da yake tsokaci game da burin gwamnatin Syria, Mr. Sabouni ya ce, babu abun da gwamnatin kasar mai ci ke maida hankali kan sa, sama da yunkurin wanzar da zaman lafiya, tare da tabbatar da cin moriyar juna tare da abokan huldar kasar, a fannonin samar da kayayyaki da na ba da hidima.
Ya ce, shawarar ziri daya hanya daya, na daya daga cikin muhimman tsare tsare dake tallafar tattalin arzikin kasar Sin da Syria tare.(Saminu)