Ministan labarai da al'adu na Najeriya, Lai Mohammed ya ce, gwamnatin kasar ta mai da hankali wajen raya wuraren bude ido na cikin gida, tare da samar da kayayyakin more rayuwa, ta yadda za a ja hankalin masu yawon bude ido na ketare.
Lai Mohammed na wannan jawabi ne yayin babban taron shekara na kungiyar masu yi wa baki jagora yayin rangadi ta kasar (NATOP) da ya gudana a Lagos, cibiyar tattalin arzikin kasar.
Ministan ya ce, har yanzu, ba a gama gano wuraren bude ido a kasar ba, la'akari da dimbin gudunmuwar da zai ba tattalin arzikin kasar.
Da yake bayyana wasu matakan da gwamnati ta dauka na raya bangaren, ya ce, ana yi wa kwamitin fadar shugaban kasa kan harkokin bude ido garambawul.
Ya ce, farfado da kwamitin zai ba da damar raya bangaren cikin gaggawa ta hanyar samar da manufofi da wasu tsare-tsare. (Fa'iza Mustapha)