in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron kolin kwararrun kasa da kasa a Beijing
2017-05-15 16:18:12 cri
An bude taron koli tsakanin kwararru da masana na kasa da kasa karo na biyar a birnin Beijing na kasar Sin, inda kwararru da masana sama da dari daga cikin gida da wajen kasar Sin suka tattauna dangane da batutuwan da suka shafi neman ci gaban duniya mai dorewa. Mahalarta taron sun bayyana cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya' za ta sanya sabon kuzari ga ci gaban harkokin fadin duniya baki daya. Mataimakin shugaban majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin Mista Chen Yuan ya halarci taron, inda kuma ya gabatar da muhimmin jawabi.

A jawabinsa Mista Chen Yuan ya ce, yana fatan taron kolin wannan karo, da ya tattaro kwararru da masana daga bangarori daban-daban, za su yi kokarin bada kyawawan shawarwari da dabaru, don kara raya "ziri daya hanya daya" da neman dauwamammen ci gaba a fadin duniya baki daya.

Kwararru da masana sun ce, dunkulewar tattalin arzikin duniya, sakamako ne na ci gaban kimiyya da fasaha, wanda ya samar da babban kuzari ga habakar tattalin arzikin duniya. A waje daya kuma, yayin da ake kokarin dunkule tattalin arzikin duniya waje daya, akwai wasu matsaloli da ake fuskanta, wadanda kamata ya yi a maida hankali kansu. Ya kamata kwararru da masana daga kasashe daban-daban, su yi nazari sosai tare da lalubo bakin zaren daidaita matsalolin da za su kawo illa ga ci gaban harkokin duniya mai dorewa, ta yadda jama'ar kasa da kasa za su ci alfanunsa.

Cibiyar mu'amalar tattalin arzikin kasa da kasa ta kasar Sin ce ta kira wannan taron koli, inda shugaban cibiyar Mista Zeng Peiyan ya halarci taron. Babban taken taron dai shi ne, tattaro hikima, da neman ci gaban duniya tare.(Murtala Zhang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China