in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta nuna damuwa game da hari kan fararen hula a CAR
2017-05-15 10:20:16 cri

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi matukar Allah wadai, game da hari kan fararen hula a janhuriyar Afirka ta Tsakiya CAR. Mr. Guterres ya yi kira ga mahukuntan kasar, da su gudanar da bincike tare da daukar matakan shari'a kan wannan lamari.

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mr. Guterres ya fitar. Sanarwar ta ce, kaddamar da hari kan jami'ar wanzar da zaman lafiya na iya zama laifin yaki. Babban magatakardar MDDr ya nuna bacin ransa bisa hare-haren ranekun 12 da 13 ga watan nan, wadanda ake zaton 'yan anti-Balaka ne suka kaddamar da su kan tawagar MINUSCA.

Ya ce, irin wannan hari na raba mutane masu yawa da muhallan su, tare da kokarin gurgunta manufar ayyukan wanzar da zaman lafiya a kasar.

Harin dai na baya bayan nan ya sabbaba kisan wani jami'in MINUSCA dan kasar Morocco daya, kuma bisa jimilla yawan dakarun tawagar da aka hallaka a kasar cikin mako guda sun kai mutane 6.

Mr. Guterres ya gabatar da sakon ta'aziyya ga iyalan jami'an MINUSCA da suka rasa rayukan su, a yayin hare-haren na kwanan nan, da ma mahukuntan kasar Morocco.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China