in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakataren MDD ya yaba yadda aka gudanar da zabe a CAR
2016-02-22 09:54:42 cri

Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya yaba da yadda aka gudanar da zabukan ranar 14 ga watan Fabrairu a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya CAR.

Mr Ban wanda ya bayyana hakan ta bakin kakakinsa, ya kuma taya Mr Faustin Archarge Touadera murnar lashe zaben shugabancin kasar kamar yadda sakamakon wucin gadi na zaben ya nunar.

Bugu da kari, Ban Ki-moon ya yabawa abokin hamayyarsa a zaben shugabancin kasar Mr Anicet Dologuele bisa ga dattakun da ya nuna na amincewa da sakamakon zaben. Sannan ya bukaci gwamnatin rikon kwaryar kasar da ta kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da zagaye na biyu na zaben 'yan majalisun dokokin kasar a kan lokaci.

Babban sakataren ya kuma nanata kudurin MDDr na ci gaba da taimakawa hukumomin wucin gadin kasar na ganin an kammala shirin mika mulkin kafin ranar 31 ga watan Maris din wannan shekara.

MDD dai ta taka muhimmiyar rawa wajen maido da zaman lafiya a Jamhuriyuar Afirka ta Tsakiya, ta hanyar tura tawagar wanzar da zaman lafiya ta MINUSCA, baya ga dakarun tsaro na gida da waje da suka sa-ido na ganin kammalar zabukan kasar cikin nasara.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China