in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ba da rahoton sabon zargin aikata fyade a CAR
2016-03-29 10:30:24 cri

MDD ta sanar da samun sabon rahoto kan zargin jami'anta dake aikin wanzar da zaman lafiya, da ma wadanda ba jami'anta ba a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya CAR.

Mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric, ya fadawa manema labaru a Litinin din da ta gabata cewar, sabon sahoton da ofishin MDD mai aikin wanzar da zaman lafiya a CAR MINUSCA, ya ce, an karbi rahoton zargin aikata fyaden ne na shekarun 2014 da 2015.

Sai dai bai bayyana adadin korafe korafen da ya karba ba.

Amma, ya bayyana wani rahoto kan zargin da akewa sojan Burundi da yin lalata da kananan yara.

Asusun yara na MDD UNICEF ya fada a makon jiya cewar, zargin na da alaka da aikata laifukan fyade kan wata yarinyua mai shekaru 14 a duniya.

Haka zalika Dujarric, ya ce, an sake samun bayanai game da sabon zargi na yin lalata wanda ya faru cikin wannan shekarar ta 2016, inda ake zargin wani sojan kasar Morocco da aikatawa, lamarin da ya kara adadin zarge zargen aikata laiffukan fyade zuwa 25 daga farkon wannan shekara.

Ya ce, wadanda matsalar ta shafa suna asibiti domin kulawa da lafiyarsu, bisa tallafin hukumar ta UNICEF.

Ana dai zargin dakarun aikin wanzar da zaman lafiya a CAR ne da laifukan aikata cin zarafi na lalata da kananan yara.

Shugaban MINUSCA Babacar Gaye 'dan kasar Senegal, ya yi murabus daga mukaminsa a watan Agustan shekarar 2015, sakamakon samun rahotannin zargin jami'an da laifukan yin lalata da kananan yara.(Ahmed Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China