in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a CAR ta yi tir da harin da aka kai wa dakarunta
2017-05-10 09:20:35 cri

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya CAR ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin da aka kai wa jerin gwanon motocinta a daren ranar Litinin.

Yayin taron manema labarai na jiya, kakakin MDD Stephane Dujarric ya ce, rahoton farko-farko ya nuna cewa, sojan kasar Cambodia 1 ya mutu, yayin da wasu sojoji 8 da suka hada da 'dan Cambodia 1 da 'yan Morocco 7 suka samu raunuka.

A wani sabon labarin kuma, Stephane Dujarric ya ce, an samu gawarwakin uku daga cikin sojojin da a baya aka ce sun bata, yana mai cewa, har yanzu, akwai raguwar guda 1 da ba a gani ba.

Kakakin MDD ya ce, tawagar ta tura sojoji domin killace wajen tare da neman wanda ya bace. Kuma tuni aka kwashe wadanda suka ji rauni inda a yanzu suke karban magani.

Tawagar wanzar da zaman lafiya na aiki kut da kut da jami'an kasar don tabbatar da kama wadanda suka farwa tawagar sojin tare da hukunta su.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China